Our Programs Lineup

Listen to Live Radio

Background

Latest Programs

close
  • 8

News

NAYI MATUKAR NADAMA AKAN HOTUNAN DANA WALLAFA ~ Bala Muhammad:Bala

Tanko Kano October 31, 2024

Muhammad, ya ba da hakuri kan tarin hutunan da ya dinga wallafawa a shafinsa na Facebook ta re da mata.Bala yana mai cewa, ya na wallafa hotunan ne don ya yi nishaɗi kawai”Nayi hutunan ne domin nishaɗi, amma ina ba da hakuri”.Bala ya bayyana hakan ne baya hukumar Hisbah ta jihar Bauchi ta gayyace shi, saboda hotunan sa da ya dinga wallafawa tare da mata daban-daban, wanda aƙalla ya wallafa hutuna kusan 50,

Read more trending_flat

close
  • 6

News

Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta gyara wutar Arewa

Maryam Farouk October 28, 2024

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya nuna damuwarsa kan matsalar da ta haifar rashin wutar lantarki a Arewacin Najeriya. Tinubu ya nuna damuwarsa kan yadda yankin ya shafe tsawon mako guda ba wutar lantarki. Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaba Tinubu, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Litinin. Shugaba Tinubu ya jagoranci ƙoƙarin gyara lalacewar wutar da ta tsayar da harkokin tattalin arziƙi a Arewa. Ya kira Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro, Nuhu Ribadu, don gyara matsalar. Lalacewar wutar, ya tsayar da al’amuran yau da […]

Read more trending_flat

close
  • 10

News

Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar dawo da wutar lantarki Arewacin Najeriya

Maryam Farouk October 28, 2024

Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce za a maido da wutar lantarki a jihohin Arewa 17 da suke fama da matsalar barna a layin Shiroro zuwa Kaduna nan da kwanaki biyar. Mista Adelabu ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan wata ganawa da yayi da shugaban kasa Bola Tinubu ranar litinin a Abuja. Ya ce matsalar wutar lantarki da ake samu a yankin Arewacin kasar nan ya biyo bayan lalata layin Shiroro zuwa Kaduna da aka yi, babban layin da ke samar da wutar lantarki ga Arewa.

Read more trending_flat

Browse By Programs